Search
Close this search box.

Gagarumar Zanga-Zangar Neman Kulla Yarjejeniyar Musayar Fursunoni Da Falasdinawa  

Yahudawan sahayoniyya sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin Tel Aviv na suna neman cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da Falasdinawa Dubban daruruwan yahudawa a matsugunan

Yahudawan sahayoniyya sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin Tel Aviv na suna neman cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da Falasdinawa

Dubban daruruwan yahudawa a matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida musamman a biranen Tel Aviv da Qudus, sun fito zanga-zangar neman a kulla yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin mahukuntansu da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa, da kuma nuna rashin amincewa da kisan wasu yahudawan sahayoniyya da ake tsare da su a Zirin Gaza sakamakon farmakin sojin haramtacciyar kasar ta Isra’ila.

Kafofin watsa labaran yahudawan sahayoniyya sun ambato majiyar ‘yan sandan haramtacciyar kasar Isra’ila tana cewa: A jiya Lahadi “Mutane akalla 100,000 ne suka halarci zanga-zangar a Kaplan a Tel Aviv.”

A halin da ake ciki kuma, jaridar yahudawan sahayoniyya ta Yedioth Ahronoth ta ruwaito masu shirya zanga-zangar da iyalan fursunonin da         ake tsare da su a Gaza na cewa: “Akalla mutane 700,000 ne suka gudanar da zanga-zanga a duk fadin kasar Falasdinu da aka mamaye, kuma adadin wadanda suka halarci babbar zanga-zangar da aka yi a Kaplan a birnin Tel Aviv sun kai mutane 550,000.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments