Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin nisa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga.
Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna.
Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe mai girma na matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta a wannan lokacin sakamako ne na nesantar koyarwar al’kur’ani, wanda kuma babu abinda hakan yake haifarwa sai rabuwar kawuna da kuma bude kafa a gaban makiya ‘yan adamtaka.”
Shugaba Fizishkiyan ya kuma ce; shi alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da dukkanin bil’adama ba tare da la’akari da launinsu ko ajinsu ba, ko kuma addinin da suke yi,kuma ya nuna wa jinsin dan’adam hanyar kai wa ga kamala.
Haka nan kuma shugaban na kasar Iran ya ce, a karkashin koyarwar addinin musulunci, mutane za su sami madogara mai karfi mai nagarta a cikin wannan duniyar da take cike da rudani.