Search
Close this search box.

Fiye Da Hafsoshin Sojin Yahudawa 800 Ne Suka Mika Takardar Yin Murabus Daga Ayyuykansu

Sama da hafsoshi sojin haramtacciyar kasar Isra’ila 800 ne suka mika takardar yin murabus daga ayyukansu a wannan shekara Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila

Sama da hafsoshi sojin haramtacciyar kasar Isra’ila 800 ne suka mika takardar yin murabus daga ayyukansu a wannan shekara

Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun watsa labari a jiya, Litinin cewa: Fiye da jami’ai sojin yahudawan sahayoniyya 800 ne masu matsayi na Kanar da Laftanar Kanal suka mika takardar yin murabus dinsu daga aiki a wannan shekara ta 2024, a wani matakin da ba a taba gani ba.

Kafafen yada labaran yahudawan sahayoniyya sun tabbatar da cewa: A yammacin jiya litinin, wani soja ya halaka, yayin da wasu 10 suka samu raunuka sakamakon harin da ‘yan gwagwarmaya suka kai musu a Gaza.

Sannan shafin yanar gizo na yahudawan sahayoniyya mai suna “Isra’ila Ba tare da Cece-kuce ba” ya tabbatar da cewa: An kashe sojan Isra’ila daya sannan wasu 10 sun jikkata, ciki har da 3 da suke cikin mawuyacin hali, sakamakon fashewar wata nakiya da aka bisine a yakin Gaza. Yayin da wani jirgin saman sojin yahudawan sahayoniyya mai saukar ungulu ya fado a safiyar jiya Litinin a kan asibitin Soroka, da ya yi sanadiyyar jikkatan sojojin yahudawan sahayoniyya masu yawa da suke yaki a Gaza.

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, sun sanar da cewa: Sun kai hare-hare kan tankokin yaki guda biyu na Merkava da wata rundunar mamayar Isra’ila tare da bindige wani sojan yahudawa a yankin Shuja’iyya a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments