Fiye Da Falasdinawa 90 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Da Su Ka Gabata

Rahotanni daga Gaza sun ambaci cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 91. Mafi

Rahotanni daga Gaza sun ambaci cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 91. Mafi yawancin shahidan dai sun kwanta dama ne sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI su ka kai musu a wuraren da aka ware na raba kayan agaji da ‘Yan Sahayoniya da Amurkawa suke tafiyar da su.

Bugu da kari, sojojin Amurka da suke a mashigar “Natasrim” sun ce; sun yi amfani da hayakin mai burkono akan fararen hulan Falasdinawa da suke gogoriyon samun abinci.

A yammacin Rafaha dake kudancin Gaza, Falasdinawa 4 ne su ka yi shahada a wurin raba kayan agaji yayin da wasu 70 su ka jikkata.

Tashar talabijin din ‘almaydin’ ta bayar da labarin dake cewa; Wani Bafalasdine guda daya ya yi shahada sanadiyyar bude masa wuta da sojojin mamaya su ka yi a mashigar “Natsrim” a yayin da yake kokarin isa inda zai sami abinci.

Shaidun ganin ido sun ce sojojin Amurka da suke a cikin wurin raba kayan agajin dake kudancin ” Natsarim” sun yi amfani da hayaki mai borkono akan fararen hula, da hakan ya sa da dama daga cikinsu su ka shake. An dauki da dama daga cikinsu zuwa asibitocin “Shuhada’ul-Aqsa’ da kuma “Audah” dake sansanin ‘yan hijira na Nusairat.

Dama dai kungiyar Hamas ta bayyana cewa; cibiyoyin raba kayan agaji da HKI da Amurka suke tafiyar da shi, ya zama wani tarko ne na kashe Falasdinawa. Kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD sun ki amincewa da su yi aiki a karkashin Amurka da HKI wajen raba kayan agajin saboda sun ce, yana da manufa ta soja da kuma korar Falasdinawa daga  gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments