Firayim Ministan Senegal Ousmane Sonko ya sanar da wani sabon shirin farfado da tattalin arzikin kasar, inda ya yi alkawarin samar da kudi “90% na aiwatar da wanann shirin ta hanyar albarkatun cikin gida da kuma kauce wa karbar bashi.
Sonko ya bayyana haka ne a lokacin da ake gabatar da wannan shiri a Dakar babban birnin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. Ya ce: “Za mu nemi haɗin kan abokan hulɗa na waje ne kawai a ɓangaren sake amfani da kadarorinmu na cikin gida.”
Ya kara da cewa “dole ne a yi amfani da kuma tattara albarkatun cikin gida don samar da mafi yawan kudaden da kasa take bukata.”
Shirin wanda ke da nufin daidaita harkokin kudi na kasar da ke yammacin Afirka, wadda ta fara hako mai da iskar gas a bara, ya zo ne a daidai lokacin da Senegal ke fuskantar kalubalen kudi da kuma tarin basusuka.
Kasar Senegal dai na fama da boyayyen bashi na biliyoyin daloli daga gwamnatin da ta shude, lamarin da ya sanya hukumar lamuni ta duniya IMF ta dakatar da shirinta na lamuni ga Senegal.