Firaministan Iraki ya yi Allah wadai da wasikar da Isra’ila ta neman yin shishigi kan Iraki

Firaministan Iraki Mohammed Shi’a al-Sudani ya yi Allah-wadai da wasikar da Isra’ila ta aike wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na bukatar daukar matakin

Firaministan Iraki Mohammed Shi’a al-Sudani ya yi Allah-wadai da wasikar da Isra’ila ta aike wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na bukatar daukar matakin gaggawa kan kungiyoyin gwagwarmayar da ke kaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan muhimman wurare a yankunan Falastinawa da Haramtacciyar kasar Isra’ila, a matsayin hujjar tabbatar da wuce gona da iri kan Iraki.

Sakon da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta aike wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yana wakiltar wata hujja ce ta cin zarafi ga Iraki da kuma yin daidai da kokarin da take yi na fadada yakin da ake yi a yankin,” in ji Sudani.

Ya jaddada kin amincewa da barazanar da gwamnatin Bagadaza ta yi wa kasarsa, yana mai cewa, Shawarwari na yaki da zaman lafiya na cikin ikon kasar Iraki ne kawai, kuma babu wata kungiya da za ta yarda ta keta wannan hakki.

Tuni dai Isra’ila ta gargadi gwamnatin Irakin da cewa muddin ba ta shawo kan hare-haren ‘yan adawa ba, to za ta fuskanci hare-haren da Isra’ila ke kaiwa yankunanta a cewar rahotanni.

Firaministan na Iraki ya kuma jaddada matsayin kasarsa na kauracewa rikici, tare da kiyaye matsayinta na neman kawo karshen rikicin Gaza da Lebanon, da kuma bayar da agaji ga al’ummar Palasdinu da na Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments