Mutum daya ne ya mutu sakamakon fashewar wata mota a gaban otal din Trump da ke jihar Las Vegas
Jami’an tsaron Amurka a jiya Laraba sun bayyana cewa: Mutum guda ya mutu kana wasu akalla bakwai suka jikkata bayan wata mota kirar lantarki ta Tesla Cybertruck ta fashe a gaban otal din Trump da ke Las Vegas.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya watsa rahoton cewa: Hukumar bincike ta tarayya a Amurka ta bayyana cewa ta shiga bincike gadanp-gadan, yayin da wasu faifan bidiyo da shaidu ganin ido daga ciki da wajen otal din suka dauka, suna nuni da yadda motar ta tashi da wuta, yayin da aka ajiye ta a wajen otal din.
Hatsarin ya faru ne sa’o’i kadan bayan wani harin da wani mutum mai tuka wata babbar mota ya kai cikin gungun masu bikin sabuwar shekara a birnin New Orleans, inda ya kashe mutane 15.
Shugaban ‘yan sandan Las Vegas Kevin McMahill ya bayyana a wani taron manema labarai cewa: “Fashewar motar Cybertruck a kusa da otal din Trump…a fili akwai tambayoyi da yawa da ya wajaba a gano amsoshinsu.