Yawan masu zanga zanga a kasar Faransa ya karu a jiya Talata a lokacin kungiyoyin kwadago malaman makarantu da daliban Jami’oii kimani 161,500 suka fito kan titunan Paris da sauran biranen kasar suna neman shugaban kasa Emmanuel Macron da firay ministansa da kuma ministan ilmi su sauka daga mukamansu. Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa yawan mutanen da suka fito sun kai 480,000.
Tashar talabijan ta Al-mayadeen na kasar Lebanon ta nakalto wakilinta a birnin Paris na cewa yawan masu zamga zanga sun ninka na sauran kwanaki a birnin, sannan bukatunsu a halin yanzu ya tashi daga neman gwamnati ta kyautata makaran kasar, zuwa neman shugaban da firay minista da ministan ilmi su sauka daga mukamansu.
Labarin ya kara da cewa yansanda da Jami’an tsaro sun yi amfani da hayki mai sa hawaye da kulake da sauran kayakin kwantar da tarzoma a kan masu zanga zanga. Wadanda muna iya cewa a halin yanzu bai takaita cikin daliban makaranta da malamansu ba, al-amarin ya game kusan dukkan sassan rayuwa na kasar.
Wasu sun ce a birnin Paris kadai mutane kimani 41,000 ne suka fito, AFP yace sun kona motoci da dama, an yi amfani da tear gas a lyon. Har’ila yau zanga zangar ta isa Nantes, Strasbourg, Toulous,Bordeaux Marseille da kuma lens, kamar yanda majiyar yansanda suka tabbatar.