Kungiyoyin kwadago a faransa na tunanin shiga yakin aiki a ranar 5 ga watan Nuwamba mai shirin kamawa a wani mataki na neman gwamnatin ta dauki mataki na magance matsalolin da suka dabaibaiye ayyukansu da kuma tsadar rayuwa.
Wannan na zuwa ne bayan jerin zanga zangar da aka gudanar a ranakun 17 da 24 ga watan Oktoba kan matsalar tsadar rayuwa da hauhawan farashin makamashi wacce ta rikide zuwa tarzoma.
Ana sa ran yajin aikin zai shafi harkokin sufuri da ilimi, yayin da Ƙungiyar Kwadago ta Ƙasa (CGT) ke son fadada yajin aikin.
Ƙungiyoyin suna bukatar tattaunawa kan albashi, daidaiton jinsi, karin kudin fansho, da mafi karancin albashi.
“Lokaci ya yi da za a dauki matakin tattara jama’a zuwa mataki na gaba; ta hanyar yajin aiki,” in ji Sophie Binet, Babbar Sakatariyar kungiyar kwadago ta CGT, bayan wani taro a Matignon da Firaminista Sébastien Lecornu a ranar 21 ga Oktoba.
Ƙungiyar ma’aikatan gwamnati ta CFDT ta shigar da sanarwar yajin aiki da ta shafi dukkan rassan ma’aikatan gwamnati guda uku.
Kafin nan dai kungiyar da ake wa lakabi da ta ‘yan Yellow Vest ta kira wani taron gangami a ranar 31 ga Oktoba.
Faransa na fama da jerin zanga zanga da ta samo asali daga fishin daliban makarantun sakandare dake nuna damuwa game da halin ko kula na gwmanatin kasar kan sha’anin ilimi a kasar.