A Faransa, an ci gaba da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a wannan Asabar, 7 ga Nuwamba, a cikin yanayi mai cike da tashin hankali, inda Ministan Harkokin Cikin Gida ya tabbatar da kama mutane 360.
Ana shirin sake yin wani yajin aiki da zanga-zanga a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, duk da matakan da aka sanya.
A wannan Asabar an kiyasta mutane 250,000 da suka shiga zanga-zanga a fadin Faransa, a cewar kungiyar hadin gwiwar matasa.
An dai jibge jami’an ‘yan sanda kimanin 70,000 a fadin kasar.
Kungiyoyin matasa da na kwadago sun kira da a kara himma wajen ci gaba da matsa wa gwamnati lamba.
Suna cewa har yanzu suna jiran martani daga gwamnati game da albashi da inganta aiki a sha’anin ilimi.
Wannan ita ce Asabar ta hudu a jere da kungiyoyi ke fitowa kan tituna a fadin kasar ta faransa, kan tsadar rayuwa, hauhawan farashin makamashi da kuma neman inganta yanayin ilimi ga matasa.
Ƙungiyoyin kwadago, daliban makarantun sakandare, daliban jami’a, da ‘yan zanga zangar da ake wa lakabi da ”Jillet jaune” sun kira jama’a da su sake fitowa kan tituna, bayan babban gangamin ranar Alhamis, 5 ga wata wanda ya hada mutane kimanin 600,000 a cewar hukumomi.