Falasdinu: ‘Yan Mamaya Sun Kama Falasdinawa 18 Da Kuma Rusa Wasu Gidaje A Yammacin Kogin Jordan

Rahotanni daga Yammacin kogin Jordan suna cewa, sojojin mamaya sun kai wasuhare-haren da kama Falasdianwa 18, bayan da su ka kutsa cikin gidajensu da gudanar

clash in nablus

Rahotanni daga Yammacin kogin Jordan suna cewa, sojojin mamaya sun kai wasuhare-haren da kama Falasdianwa 18, bayan da su ka kutsa cikin gidajensu da gudanar da bincike. Haka nan kuma rahotannin sun ce, ‘yan sahayoniyar sun lalata kayan da suke a cikin gidajen da su ka kutsa.

A wani gefen sojojin mamaya sun shiga cikin sansanin “Balata” sannan kuma su ka killace titin Qudus a garin Nablus, da kuma kafa wuraren bincike akansa.

Majiyar ta kuma ce, sojojin mamayar sun aike da jiragen sama marasa matuki suna shawagi a samaniyar sansanin na “Balata” a daidai lokacin da ake jink arar bude wuta da fashewar abubuwa masu karfi.

A unguwar “Suq” dake cikin sansanin sojojin mamayar sun kutsa cikin wani gida inda su ka kamo wani matashi a cikinsa.

Da safiyar yau Talata sojojin na mamaya sun janye da asuba daga birnin Nablus, bayan da su ka kama wani matashi Bafalasdine a titin “al-Ittihad”.

Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta kasar Qatar ta bayar da labarin dake cewa; sojojin mamaya sun fara rushe gidajen Falasdinawa a garin “Deir-Balut” a gundumar Silfit a arewa da yammacin kogin Jordan.

Haka nan kuma sojojin na Isra’ila sun aike da motocin yaki zuwa cikin kauyen Anza a kudancin birnin Jenin, tare da manyan motocin rusau na soja, inda su ka fara rushe wani bene mai hawa biyu da kuwa wani wurin shan Coffee na mashigar garin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted