Falasdinawa Suna Komawa Muhallinsu Bayan Tsagaita Bude Wuta A Zirin Gaza

Dubban Falasdinawa da suka rasa matsugunansu suna komawa birnin Rafah daga gudun hijira tsawon watanni Sa’o’i kadan kafin yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza ta

Dubban Falasdinawa da suka rasa matsugunansu suna komawa birnin Rafah daga gudun hijira tsawon watanni

Sa’o’i kadan kafin yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza ta fara aiki, dubban Falasdinawa mazauna birnin Rafah suka fara komawa gidajensu, inda wasu daga cikinsu suka rushe, wasu kuma bangarorinsu suka lalace bayan dandana kudarsu a lokacin gudun hijira.

Wakilin gidan talabjin na Al-Alam na kasar Iran a Rafah Mohammed Abu Obeid, ya bayyana cewa: Dubban Falasdinawa da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka raba da gidajensu da yankunansu, sun fara komawa gidajen nasu da yankunansu a birnin Rafah.

Dan rahoton ya bayyana cewa: Bayan tsawon watanni 8 da tilastawa dubban Falasdinawa dakauracewa muhallinsu, dubban Falasdinawa sun kwarara zuwa cikin birnin na Rafah domin ganin halin da gidajensu suke ciki, inda wasu suka tarar da gidajensu a rushe, wasu sun lalace tare da tarar da gawarwakin ‘ya’yansu, wadanda yawancinsu ba a binne su ba.

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Zirin Gaza ta fara aiki ne da safiyar yau Lahadin nan, a daidai lokacin da ake fatan kawo karshen hare-haren bama-bamai da kisan kiyashin da sojojin yahudawan sahayoniyya suka yi na tsawon kwanaki 470 kan mazauna yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments