Jiragen yakin HKI sun cilla makamai a kan makarantar Mustafa Hafez inda falasdinawa kimani 700 suke samun mafaka a cikinta a zirin Gaza. Labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu a wannan harin yara ne.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar asbitoci a yammacin zirin gaza na cewa an kashe Falasdinwa akalla 20 kuma mai yuwa yawan wadanda suka yi shahada ya karu saboda irin mummunan raunukan da wasu Falasdinawa suka ji a wannan harin.
Labarin ya kara da cewa makamai masu karfi, wadanda sojojin yahudawan suka cilla kan makarantar ya rugurguzata ta gaba daya.
Har’ila yau a safiyar yau Laraba, mutane 6 ne aka tabbatar da shahadarsu a wasu hare-haren yahudawan suka kai garin Buraij inda falasdnawa da dama suke samun mafaka a yammacin gaza.