Search
Close this search box.

Espaniya Ta Mika Bukatarta Ta Shiga Cikin Shari’ar Da Afirka Ta Kudu Ta shigar A Gaban Kotun ICJ Na Tuhumar HKI Da Kissan Kare Dangi A Gaza

Bayan ta amince da kasar Falasdinu a matsayin kasa mai zaman kanta, gwamnatin kasar Espania ta gabatar da bukata ga kotun kasa da kasa ta

Bayan ta amince da kasar Falasdinu a matsayin kasa mai zaman kanta, gwamnatin kasar Espania ta gabatar da bukata ga kotun kasa da kasa ta ICJ don shiga cikin shari’ar da kasar Afirka ta Kudu ta shigar a gaban kotun na zargin HKI da aikata kissan kiyashi a zirin gaza na kasar falasdinu da aka mamaye.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalti ministan harkokin wajen kasar Espania Jose Manuel Albares yana fadar haka a yau Alhamis.

Ya kuma kara da cewa kasarsa ta dauki wannan matakin ne don ganin har yanzun HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, wanda mafi yawan kasashen duniya sun tabbatar da cewa laifin yaki ne wanda yakamata kotun ta kasa da kasa ta shiga tsakani.

Albares ya kara da cewa “kasar Espaniya ta damu da yadda yakin Gaza yake kara fadada a yankin gasa ta tsakiya’ . Ya ce kasar Espaniya tana son ganin zaman lafiya ya dawo a Gaza, da kuma gabas ta tsakiya, da kuma ganin an aiwatar da dokokin kasa da kasa dangane da wannan rikicin.

Ya kammala da cewa kasar Espaniya ta dauki wannan matakin ne don kawo karshen yakin da kuma dawowa kan hanyar da ta dace na warware wannan rikincin wanda kasashen duniya suka amince das hi wato samar da kasashe biyu.

Gwamnatin kasar Espaniya ta bayyana haka ne mako guda kacal da ta shelanta amincewa da kasar Falasdinu mai cikekken yenci a kan kasar falasdinu da aka mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments