Duniya Na Yin Tir Da Kazamin Harin Isra’ila Kan Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Rafah

Kasashe da hukumomin kasa da kasa na ci gaba da mayar da martani kan kazamin harin da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira

Kasashe da hukumomin kasa da kasa na ci gaba da mayar da martani kan kazamin harin da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Rafah wanna ya yi sanadin mutuwar gwamman mutane ciki har da mata da yara.

A martaninta fadar gwamnatin Amurka, (White House), ta bukaci Isra’ila da ta dauki duk wani mataki na kare fararen hula a Gaza.

Shi kuwa Babban jami’in hulda da kasashen waje na Tarayyar Turai, Josep Borrell, ya bukaci Isra’ila da ta bi umarnin Kotun Duniya na makon da ya gabata na ta daina kai hari a Rafah.

Iran ta bakin, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kan’ani ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, yana mai kira da a mayar da martani a aikace da kuma tofin Allah tsine daga kasashen duniya.

Hukumar Falasdinawa ta yi Allah-wadai da lamarin inda ta ce kisan kiyashin da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi, kalubale ne ga dukkan kudurorin halaccin kasa da kasa,”

Babban jami’in Hamas Sami Abu Zuhri ya kira harin a matsayin “kisan kiyashi” yana mai cewa Amurka ce ke da alhakin taimakawa gwamnatin Isra’ilar.

Qatar ta ce harin babban cin zarafi ne ga dokokin kasa da kasa da zai kara tsananta matsalar jin kai a Gaza.

Harin na iya kawo cikas ga kokarin shiga tsakani na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce kasarsa za ta yi “dukkan mai yiwuwa” don ganin an kama shugaban gwamnatin masu kisan dabbanci, Benjamin Netanyahu, game da munanan hare-haren.

Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bi sahun masu yin Allah wadai da lamarin, inda suka yi kira ga kasashen duniya da su sa baki cikin gaggawa.

Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya yi gargadin cewa sam ba za a amince da tabarbarewar yanayin jin kai a Gaza ba.

Jordan ta kuma yi Allah wadai da laifukan yaki da sojojin mamaya na Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce “Wannan matakin ya sabawa hukuncin kotun kasa da kasa kuma ya zama babban cin zarafi ga dokokin kasa da kasa da kuma dokokin jin kai.”

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ya fusata kan hare-haren da gwamnatin Isra’ilar ta kaiwa Falasdinawa da suka rasa matsugunansu.

“Dole ne a dakatar da wadannan ayyukan. Babu wani wuri mai aminci a Rafah ga fararen hula Falasdinawa,” in ji Macron a kan shafin ”X” .

Ya bukaci cikakken mutunta dokokin kasa da kasa da kuma tsagaita bude wuta nan take.”

Masar ta kuma yi Allah wadai da harin da aka kai a sansanin da gangan, tana mai kira ga Isra’ila da ta aiwatar da matakan da kotun kasa da kasa (ICJ) ta umarta.

Ministan harkokin wajen Spain Jose Manuel Albares ya ce harin bam da aka kai a Rafah ya kasance “kwana daya da kashe fararen hula Falasdinawan da ba su ji ba ba su gani ba.”

Mummunan harin, ya yi girma” saboda ya zo ne bayan umarnin ICJ da ya umarci gwamnatin da ta dakatar da kai hare-hare a Rafah.

Ministan harkokin wajen Ireland, Micheal Martin, ya bayyana harin a matsayin wata ” barna.”

Kuma takwaransa na kasar Norway Espen Barth Eide ya bayyana hare-haren a matsayin “keta hukuncin kotun koli ta duniya.”

 “Ya zama wajibi. Ya zama dole,”in ji shi yayin da yake magana kan umarnin ICJ na dakatar da hare-haren Rafah.

Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat shi ma ya yi Allah wadai da harin a cikin wani sako da ya aike ta X. Isra’ila na ci gaba da keta dokokin kasa da kasa ba tare da wani hukunci ba, tare da raina hukuncin da kotun ICJ ta yanke kwanaki biyu da suka gabata na bayar da umarnin kawo karshen ayyukan soji a Rafah.

A ranar Juma’a ne kotun kasa da kasa ta umarci Isra’ila da ta dakatar da kai hare-hare a Rafah.

Kungiyar kare hakkin Yahudawa ta Voice for Peace ta kuma bukaci a kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza.

 “Ba za mu taba mantawa da hotunan da ke fitowa daga Rafah a daren yau ba.

An kona mutane da suka hada da jarirai da ransu tare da tarwatsa su. Dole ne a kawo karshen wannan kisan kiyashi, dole ne a kawo karshen hakan a yanzu.”

Kungiyar da ke da mazauni a Amurka ta ce ta dora alhakin lamarin kan goyan bayan da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden, ke ba Isra’ila, wanda ya yi sadadin mutuwar Falasdinawa sama da 36,000.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments