Dubban mutane a birnin London sun yi cincirindo a kofar shiga sansanin sojojin sama da ke arewa maso yammcin birnin London inda suke zargin gwamnatin kasar da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jiragen yakin F-35 na kasar Burtania suna shawagi a tekun medeteranin inda suke taimakawa HKI yakin da take fafatawa da Falasdinawa a Gaza. Don haka gwamnatin kasar tana da hannui a kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza.
Tun cikin watan octoban shekara da 2023 mutane daga bangarori daban-daban a kasar Burtaniya suke zanga-zanga don neman a kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa a Gaza, sannan a bawa kasar falasdinu cikekken yanci bayan shekaru 76 na mamaya da mulkin mallaka da kissan kiyashi.
A ranar Asabar da ta gabata ma yansanda a kasar Burtaniya sun kama mutane fiye da 60 saboda sun fito zanga-zanga na goyon bayan Falasdinawa karkashin kunyar Free Palastine’ wacce gwamnatin kasar ta dauka a matsayin ta yan ta’adda.