A Isra’ila Kwanaki uku kafin zaben ‘yan majalisa, dubban mutane sun yi zanga-zanga a Tel Aviv ranar Asabar kan gwamnatin Benjamin Netanyahu.
Zaben ‘yan majalisa da aka fi sani da kuri’ar raba gardama kan Benjamin Netanyahu, gabaninsa dubban mutane sun taru a Tel Aviv, don yin zanga-zanga a kan gwamnatin Isra’ila.
Kungiya da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a hare-haren ranar 7 ga Oktoba, na daga cikin wadanda suka shiga zanga zangar.
Kungiyar na mai neman a kafa kwamitin bincike kan gazawar gwamnatin Netanyahu wajen shawo kan lamuran tsaro da ya ba wa Kungiyar Hamas ta Falasdinawa damar kai harin, wanda shi ne mafi muni a tarihin kasar.
Gwamnatin Benjamin Netanyahu ta ki amincewa da irin wannan kwamiti, duk da kiran da Isra’ilawa da yawa suka yi mata.
Kafin nan dai manyan ‘yan adawa da suka tsaya takara a zaben na ranar Talata, na farko kuma tun bayan harin na ranar 7 ga Oktoba, 2023 – duk sun yi alkawarin aiwatar da bincike idan suka yi nasara.