Dubban mayaka ‘yan gwagwarmaya a Iraki na shirye domin marawa Hezbollah baya

Wani bangare na ‘yan gwagwarmayar Iraki ya yi alkawarin bayar da dubban mayakansa domin mara baya ga kungiyar Hizbulllah ta kasarr Lebanobn wajen tunkarar ayyukan

Wani bangare na ‘yan gwagwarmayar Iraki ya yi alkawarin bayar da dubban mayakansa domin mara baya ga kungiyar Hizbulllah ta kasarr Lebanobn wajen tunkarar ayyukan  ta’addanci na haramtacciyar kasar Isra’ila a kan Labanon.

Sakatare-janar na dakarun Kataib Sayyed al-Shuhada, Abu Alaa al-Walai, ya ce dubban ‘yan kasar za su kasancea  cikin a cikin cikakken shiri” idan babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sayyed Hassan Nasrallah ya ba da umarni.

Shugaban kungiyar Kataib ya rubuta a cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Hizbulah a ranar Laraba cewa, “Mu da  makamanmu da dukiya, da rayukanmu, sojoji ne da suka yi cikakken shiri a karkashin jagorancin ku.”

“Idan kun rasa shahidai dubu, za mu samar muku da mayaka jarumai dubu dari. Kuma Allah shi ne shaida a kan abin da muke fada,” in ji al-Walai.

Ya kuma kara jaddada wajabcinhadin kai tsakanin dukkanin kungiyoyin gwagwarmaya na yankin gabas ta tsakiya,  yana mai cewa , mayakan gwagwarmaya a Iraki a shirye suke su cika fagen yaki a Lebanon idan akwai bukata.

Sayyid Nasrallah ya yi magana a ranar Alhamis inda ya tabbatar da cewa kungiyar gwagwarmayar Gizbullah na ci gaba da samun karfin fagen daga, yayin da mayakan kungiyar suka kaddamar da hare-hare 17 a kan wurare na sojojin Isra’ila, da hakan ya hada da wurare na leken asiri da tattara bayanan sirri na sojin Isra’ila, inda Hizbullah tav samu nasarar halaka wasu daga cikin sojojin yahudawan Isra da kuma jikkata wasu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments