Tashar talabijin din “Kan 11” ta yi hira da daya daga cikin ‘yan ta’adda da su ka kai wa garin Halab na Syria hari, inda ya bayyana cewa; “ Wadanda ya kamata ku ji tsoronsu su ne Basshar, Iran da Hizbullah, amma ba mu ba.”
Tun kwanaki biyu da su ka gabata ne dai kafafen watsa labarun na HKI su ka mayar da hankali wajen daukar labarun da suke da alaka da hare-haren da ‘yan ta’adda na kungiyar “Tahrirus-sham’ da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai.
Shi kanshi shugaban hukumar Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya yi zaman na musamman da ‘yan majalisar gwamnatinsa, inda su ka tattauna abubuwan da suke faruwa a kasar Syria.
Wannan tashar talabijin din wacce ta watsa hirar da ta yi da daya daga cikin ‘yan tawayen na Syria mai suna Suhail Hammud, wanda ake yi wa kinaya da “Abu Tawi” ya ce; Basshar Asad, Iran da Hizbullah su ne ya kamata ku rika jin tsoronsu,amma ba mu ba.”
Tashar talabijin din ta Kan 11 ta ce, abinda Hammud ya fada yana bai wa Isra’ila tabbacin zaman lafiya da su.
Hammud ya kuma fadawa Isra’ilawa cewa: Sakona gare ku shi ne kar ku damu da cewa Iran da Hizbullah za su iya yi mana wani abu, za mu yi maganinsu. Ku ne ya kamata ku ji tsoron Basshar Asad, Iran da Hizbullah, domin sun fi masu “ Kishin musulunci” zama abin tsoro.
Tashar talbijin din Kan ta kuma bayyana cewa; Isra’ila tana sa ido akan abinda yake faruwa a tsakanin shugaba Assad da kuma ‘yan tawaye da yadda abubuwa suke tafiya a kasar.