Darare Biyu A Jere Makaman Yemen Na Faduwa Kan Tel’aviv, Miliyoyi Sun Ruga Zuwa Mafaka

A karo na biyu a jere, makamai masu linzami samfurinBilistic Sun Fada Kan Birnin Telaviv babban birnin HKI, inda miliyoyi yahudawa suka ruga zuwa wuraren

A karo na biyu a jere, makamai masu linzami samfurinBilistic Sun Fada Kan Birnin Telaviv babban birnin HKI, inda miliyoyi yahudawa suka ruga zuwa wuraren buya, amma duk da haka wasu mutane kimani 9 sun ji rauni.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar HKI tana bayyana haka, ta kuma kara da cewa a sanyin safiyar yau Laraba ce, jiniyoyin gargadi suka tashi a cikin birnin, a dai-dai lokacinda makamai mai linzami na kasar Yemen sun tunkari birnin bayan ya cinya tazarar kilomita fiye da 2000 kafin ya isa birnin.

Hukumar kwana-kwana ta HKI ta ce sun baza ma’aikatansu zuwa wurare da dama don taimakawa wadanda suka ji rauni ko kuma suke bukatar taimakon su.

Wannan shi ne karo na biyu a jere, sojojin yemen suke cilla makamai masu linzami kan birnin telaviv. Majiyar ta kara da cewa an ji karar tashin jiniya a wurare kimanin 200 a cikinn birnin. Majiyar ba ta bayyana asararin da HKI ta yi sanadiyyar faduwar makamin ba.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments