Search
Close this search box.

Daraktan Hukumar UNRWA Ya Ce: An Raba Yaran Falasdinawa Da Dabi’arsu Ta Kuruciya Saboda Da Yaki

Babban daraktan Hukumar ba da Agaji da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ga ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ya ce: Hare-hare sun raba yaran Gaza da matsayinsu

Babban daraktan Hukumar ba da Agaji da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ga ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ya ce: Hare-hare sun raba yaran Gaza da matsayinsu na kuruciya

Babban daraktan Hukumar Ba da Agaji da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ga ‘yan gudun hijirar Falasdinawa Philippe Lazzarini, ya ce hakika ayyukan ta’addancin da ake aiwatarwa kan al’ummar Falasdinu sun yi sanadiyyar raba yaran Gaza da dabi’arsu ta kuruciya.

Cibiyar yada labaran Falasdinu ta nakalto bayanin Lazzarini yana jaddada cewa a wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin “X” cewa: Tabbas yara a Zirin Gaza sun shiga wani mummunan hali da babu wani yaro a duniya da ya kamata ya gani ko ya dandani makamancinsa. An kashe da yawa daga cikinsu, kuma da dama daga cikinsu sun fuskanci raunuka da suka gurbata musu halitta da zasu kasance cikin nakasa har tsawon rayuwarsu.

Ya ci gaba da cewa: Wadanda suka tsira daga cikin yaran suna fama da mumanan raunuka. Sannan an lalata makarantunsu kuma sun yi hasarar duk shekarun da suka yi a makaranta, babu batun walwala ko wasa a fagen rayuwarsu.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka fara kaddamar da farmaki kan zirin Gaza ta kasa da ruwa da kuma ta sama, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 37,232 wadanda akasarinsu yara da mata ne, yayin da wasu 85,037 suka jikkata, kuma dubbai suna karkashin baraguzan gine-gine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments