Iran: Imam Sayyid Aliyul Khamnae Ya Ce Ayyukan Hajji Na Tada Hankalin Makiya Musulmi A Dinuya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa ayyukan hajji, da taron musulmi a wurare masu tsarki a kasar Hijas yana tada hankalin makiya a duniya. Jagoran ya bayyana haka ne a sakonsa ga musulmi, musamman mahajjan bane, wanda za’a karanta cikekken sakon a madadinsa a filin Arafa a gobe Asabar. […]
Iran Ta Ce, HKI Zata Fada Cikin Jahannama Idan Ta Yi Kokarin Mamayar Kasar Lebanon

Mukaddashin ministan harkokin wajen JMI Ali Bakiri Kani ya bayyana cewa, HKI zata jefa kanta cikin Jahannam idan ta kuskura ta farwa kasar Lebanon da yaki da nufin mamayarta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Bakiri Kani yana fadar haka a lokacinda yake jawabin hadin giwa da Qasim Al-Araji mai bawa firaiministan […]
Aya.Ahmad Khatami Ya Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da Aka Yi A Kasar Sudan

Limamin masallacin jumma’a a nan birnin Tehran ya yi allawadai da kissan kiyashin da ake yi a kauyukan kasar Sudan. Tashar talabjin ta Labarai a nan Tehran ta nakalto limamin yana fadar haka a khudubarsa ta biyu a sallar Jumma’an da ya jagoranta a jami’ar Tehran. A yau kimani shekara guda Kenan da fara yakin […]
Dakaru Masu Gwagwarmaya A Gaza Sun Ci Gaba Da Fafatawa Da Sojojin HKI A Rana Ta 252 Da Fara Yakin Tufanul Aksa

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto yan rahotanninta daga Gaza suna cewa a ranar ta 252 da fara yakin Tufanul Aksa, dakarun Saraya Kudus na kungiyar Jihadul Islami sun cilla makamai kan sojojin HKI a garin Rafa da ke kudancin ga kan iyaka da kasar Masar. Labarin ya kara da cewa dakarun […]
Dakarun Kungiyoyin Musulmi A Iraki Sun Cilla Makaman Drones Kan Wani Sansanin Sojojin Sana Na HKI A Safiyar Yau Jumma’a

Dakaru masu gwagwarmaya da yan ta’adda a kasar Iraki sun bada sanarwan cilla makaman Drons kan sansanin sojojin sama na HKI a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto wani bayanin da kungiyoyin suka fitar a safiyar yau jumma’a na cewa sun cilla makaman drons kan sansanin […]
Ali Baqiri Ya Ce: Idan Yahudawan Sahayoniyya Suna Da Hankali Ba Zasu Sake Shiga Yaki Da Lebanon Ba

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Kasar Lebanon za ta zama jahannama ga yahudawan sahayoniyya da ba zasu taba tunanin sake mamaye ta ba Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri ya yi nuni da cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su dauke da wasu kyawawan abubuwan tunawa a kasar Labanon, kuma hanyar rugujewar […]
Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula A Yakin Da Ake Yi A Sudan

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a Sudan Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya yi Allah wadai da kisan gilla da kuma raunata daruruwan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba […]
Daraktan Hukumar UNRWA Ya Ce: An Raba Yaran Falasdinawa Da Dabi’arsu Ta Kuruciya Saboda Da Yaki

Babban daraktan Hukumar ba da Agaji da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ga ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ya ce: Hare-hare sun raba yaran Gaza da matsayinsu na kuruciya Babban daraktan Hukumar Ba da Agaji da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ga ‘yan gudun hijirar Falasdinawa Philippe Lazzarini, ya ce hakika ayyukan ta’addancin da ake aiwatarwa kan al’ummar […]
Wasu Mata Uku Da Karamin Yaro Sun Yi Shahada Sakamakon Harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Wasu mata Falasdinawa uku da wani yaro daya sun yi shahada sakamakon harin bam da yahudawan sahayoniyya suka kai a Gaza Majiyoyin cikin gida a Falasdinu sun watsa rahoton cewa: Wasu mata guda uku da wani karamin yaro sun yi shahada sakamakon luguden bama-bamai da jirgin saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi kan […]
Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Jiragen Ruwan Da Suke Taimakawa Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai farmakin soji guda uku a tekun Bahar Maliya kan jiragen da suke kai tallafi ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e a jiya Alhamis ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin din kasar cewa: Farmakin farko da sojojin Yemen […]
Zanga zangar Goyan Bayan Falasdinu A Yayin Bude Taron Kolin G7

An fara taron koli na kwanaki uku na kungiyar G7 na shekara ta 2024 a cikin zanga-zanga, a Borgo Egnazia, wani wurin shakatawa dake kusa da garin Fasano a kudancin yankin Apulia na kasar Italiya. Rikicin Ukraine da na Gabas ta Tsakiya da kuma dangantakar dake tsakanin kungiyar da kasashe masu tasowa su ne batutuwan […]
Iran : Ana Ci Gaba Da Yakin Neman Zaben Shugaban Kasar

A Iran, ‘yan takara shida da zasu fafata a zaben shugaban kasar na ranar 28 ga watan Yunin nan na ci gaba da yakin neman zabe. Zaben dai za’ayi shi ne shekara guda kafin lokacin da ya kamata a gudanar da shi sakamakon rasuwar shugaban kasar Ebrahim Ra’asi da wasu mukarabansa a yayin wani hatsarin […]
Isra’ila Na Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Zirin Gaza A Daidai Lokacin Da Ake Dakon Sasantawa

Isra’ila, na ci gaba da kai hare-hare a Gaza, a daidai lokacin da ake dakon fatan samun sasantawa. Fadan dai ya fi karkata ne a yankin Rafah da ke kudancin Falasdinu, inda a farkon watan Mayu sojojin Isra’ila suka kaddamar da hare-hare ta kasa. Bayanai sun ce ko a jiya an yi musayar wuta sosai […]
Hamas Ta Yi Watsi Da Sukar Amurka Kan Jan Kafa Wajen Amincewa Da Kudirin Tsagaita Wuta

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mayar da martani ga suka daga Amurka dangane da jan kafa wajen amincewa da kudurin tsagaita bude wuta. Hamas dai na mayar da martini ne kankalamman sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na cewa it ace ke jan kafa wajen amincewa da kudirin da MDD, ta amince da shi. […]
Iran Ta Jadadda Wajabcin Sassauta Rikice-rikice A Yankin

Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ta jaddada wajabcin sassauta rikici da warware rikice-rikice a yammacin Asiya. Mista Kani, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai na hadin guiwa da takwaransa na Iraki Fuad Hussein a birnin Bagadaza ranar Alhamis. Yana mai cewa ‘’kasashen biyu masu […]