Search
Close this search box.

Dan Shahidi Isma’il Haniyeh Ya Jinjinawa Al’ummar Yemen Kan Tallafawa Falasdinawa

Dan shahidi Isma’il Haniyah ya bayyana cewa: Al’ummar Yemen sun tallafa wa Falasdinawa da jininsu da daukakarsu Rahotonni sun watsa faifan bidiyo na dan shahidi

Dan shahidi Isma’il Haniyah ya bayyana cewa: Al’ummar Yemen sun tallafa wa Falasdinawa da jininsu da daukakarsu

Rahotonni sun watsa faifan bidiyo na dan shahidi kuma kwamandan gwagwarmayar Musulunci Ismail Haniyeh, wato Abdul Salam Haniyeh, inda yake yabawa al’ummar kasar Yemen kan tsayin daka da goyon bayan al’ummar Falasdinu a Zirin Gaza.

Dan shahidin Abdul-Salam Haniyeh ya jaddada godiya ga al’ummar Yemen, wadanda suke tallafa wa Falasdinawa da jini, da daukakarsu, inda ya maimaita har sau biyu.

Haka nan kuma ya mika godiyarsa ga goyon baya da ‘yan gwagwarmayar kasashen Lebanon da Iraki, wadanda suka tsaya tsayin daka a kan tallafa wa ‘yan gwagwarmayar Gaza a lokacin da suke cikin mawuyacin hali sakamakon zaluncin yahudawan sahayoniyya da tafka laifuffukan kisan kiyashi da ba a taba ganin irinsa ba a tsawon tarihi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments