Dan kasar Iran Ya Zama Zakaran Asiya  Na 2024 A Fagen Dambe A Tsakanin Daliban Makaranta  

Dan wasan damben zamani dan kasar Iran Farzan Ahmadi Afzahi ya zama zakara a tsakanin dalibai ‘yan makaranta a shekarar nan mai karewa ta 2024.

Dan wasan damben zamani dan kasar Iran Farzan Ahmadi Afzahi ya zama zakara a tsakanin dalibai ‘yan makaranta a shekarar nan mai karewa ta 2024.

Hukumar wasan damben zamani ta nahiyar Asiya ce ta sanar da Farzan Ahmadi Afzadi a matsayin zakara na wannan sherkara ta 2024 mai karewa.

A jiya Lahadi ne dai hukumar ta yi wannan sanarwar bayan nazarin yadda Ahmadi din ya gudanar da wasanninsa na dambe na matasan maza da mata wanda aka yi a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Dan wasan na Iran ya yi gasarsa ne a cikin ajin nauyi 61, da ya nuna kwazo a cikin raga akan abokan hamayyarsa.

Iran tana samun lambobin yabo a cikin fagage mabanbanta na wasanni a cikin nahiyar Asiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments