Search
Close this search box.

Dakarun Sarayar Al-Quds Sun Nuna Yadda Suka Harbor Jirgi Maras Matuki Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Dakarun Sarayar Al-Quds bangaren sojin sojin kungiyar Jihadul-Islami na Falasdinu sun nuna wani faifan bidiyo da ke nuna yadda suka harbo wani jirgin sama maras

Dakarun Sarayar Al-Quds bangaren sojin sojin kungiyar Jihadul-Islami na Falasdinu sun nuna wani faifan bidiyo da ke nuna yadda suka harbo wani jirgin sama maras matuki ciki na ghwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kirar “EVO MAX 4T a sararin samaniyar birnin Khan Yunus da ke Zirin Gaza.

A gefe guda kuma, kafar yada labaran bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas na Izzuddeen al-Qassam ta watsa wani faifan bidiyo da ke nuna yadda mujahidanta ke harba makamai masu linzami kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila. Kamar yadda a nata bangaren, rundunar sojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa an kashe sojojinta biyu tare da jikkata wasu hudu a yakin da suke yi da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a kudancin Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments