Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare juya halin Musulunci na kasar iran IRGC sun sanar da kama jiragen ruwa guda biyu da ake fasakwaurin mai da su a kusa da tsibin farisa, dake tekun fasha, kuma sun kama jiragen ne a yayin wani sintiri da suka gudanar kuma sun kama jiragen yana dauke da litar mai miliyan 1 da aka sata.
rahoton ya kara da cewa ana tsare da matukan jiragen ruwan guda 15 kuma an mika su zuwa ga bangaren sharia domin daukar matakin sharia da ya dace a kansu, kuma jiragen an nuna cewa sun dade suna aiki karkashin wata cbiyar masu fasakwabri na tsawon watanni.
Iran ta kara himma wajen dakile fasa –kwabrin albarkatun mai a tekun fasha , ana jigilar kayayyakin mai na mota ba bisa ka’ida ba zuwa kasashen larabawa dake yankin inda farashin mai zai iya ninka na cikin iran sau 20.