Manjo Janar Ali Fadavi, mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ‘IRGC’, ya ce: An kara shirya dakarun “IRGC” cikin watanni biyu da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Manjo Janar Fadavi ya ce tun kafuwar “IRGC” har zuwa yau, inganta karfin yakin “IRGC” ya kasance abu mai muhimmanci kuma bai taba tsayawa ba.
Ya kara da cewa: “A cikin yakin kwanaki 12 da aka dora wa Iran, mutane sun ga karuwar karfin yaki da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na “IRGC” suka samu a fagen kalubalantar makiya.”
Manjo Janar Fadavi ya jaddada cewa: Shirye-shiryen dakarun “IRGC” a yau ya zarce na watanni biyu da suka gabata.