Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Suna da shirye-shiryen tunkarar jiragen saman yakin makiya kirar F22 da F35
Kwamandan rundunar tsaron sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya tabbatar da cewa: Iran na da kwakkwaran Shirin iya tunkarar jiragen saman mayakan kirar F22 da F35.
A cikin wata sanarwa da ya aikewa gidan talabijin na Iran a yammacin jiya Alhamis, kwamandan rundunar tsaron sararin samaniyar sojojin saman Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Sheikhian ya bayyana cewa: Bayan nasarar da aka samu na tsarin D9 a cikin ayyukan hadin gwiwa na hukumar tsaron sararin samaniyar kasar, adadi mai yawa na wannan tsarin zai kasance tare da sojojin tsaron sararin samaniyar kasar.
Ya ci gaba da cewa: Nasarar da wannan tsari ya samu tare da tsare-tsare irin su Dezful da Sobame-Khordad a atisayen sojin hadin gwiwa na hukumar tsaron sararin samaniyar kasar ya nuna cewa: Ikrarin lalata tsaron sararin samaniyar Iran da yahudawan sahyoniya suka yi, karya ce tsagwaronta. Kuma Iran tana da shirye-shiryen tunkarar jiragen saman mayakan kirar F22 da F35, kuma nan ba da jimawa ba za su ga karin na’urar makami mai linzami da za a yi amfani da shi wajen tsaron sararin samaniyar kasar ta Iran.