Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun rusa wata hanyar sadarwar leken asiri a lardin Khuzestan da ke kudu maso yammacin Iran
Jami’an leken asiri na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a lardin Khuzestan dake kudu maso yammacin kasar Iran sun samu nasarar cafke wasu jami’an leken asiri da suke aiki da hukumar leken asiri ta daya daga cikin kasashen yankin tekun Fasha.
Ma’aikatar hulda da jama’a ta Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran IRGC ta “Waliyul- Asr (Allah Ya gaggauta bayyanarsa)” a lardin Khuzestan ta watsa rahoton cewa: Dakarunta sun samu nasarar wargaza wata kungiyar leken asirin da ke aiki da hukumar leken asirin kasashen waje a jiya Juma’a sakamakon kokarin da Dakarun suke yi dare da rana a lardin na Khuzestan.
Ma’aikatar ta kara da cewa: An kama ‘yan kungiyar leken asirin da ke aiki da hukumar leken asiri ta daya daga cikin kasashen yankin tekun Fasha, kuma Dakarun kare juyin jya halin suna aiki da himma wajen tattara bayanai daga wasu cibiyoyi masu muhimmanci a lardin, inda suka mika ‘yan leken asirin ga hukumomin shari’a da suka cancanta.