Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci  Sun Bayyana Cewa: Masu Shirin Halaka Gaza Suna Son Mamaye Duniyar Musulmi Ne

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Masu shirin halaka Gaza suna neman hadiye duniyar Musulunci  ne Dakarun kare juyin juya

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Masu shirin halaka Gaza suna neman hadiye duniyar Musulunci  ne

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci nanIran sun yi gargadin cewa; Bangarorin da ke shirya kisan kiyashi a Gaza ba wai kawai halakar al’ummar Falastinu ba ne kawai, a’a suna neman mamaye yankuna masu arziki da muhimmanci na duniyar Musulunci ne a wani bangare na ci gaba da fadada ayyukan da suka shafi tsaro da albarkatun kasa.

Dakarun kare juyin juya halin na Musuluncin sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Tsayin daka da gwagwarmayar da al’ummar Falastinu suke yi a yau a zirin Gaza wajen fuskantar kisan kare dangi da laifukan yahudawan sahayoniyya, wata shaida ce da ke nuni da irin sadaukarwar da wannan al’umma take da shi na ‘yantar da Falastinu da Qudus mai tsarki, da kuma ci gaba da tafarkin shahidi mai girma Isma’il Haniyyah – tsohon shugaban bangaren siyasar kungiyar Hamas da sauran shahidan ‘yar gwagwarmayar wajen fuskantar ‘yan sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted