Dakarun Kai Daukin Gaggawa Na Kasar Sudan Suna Ci Gaba Da Aikata Laifukan Yaki A Kasar

Al’ummar Sudan da suka rasa matsugunansu na fuskantar cin zarafi mafi muni daga Dakarun kai daukin gaggawa na kasar Wasu ‘yan gudun hijira da suka

Al’ummar Sudan da suka rasa matsugunansu na fuskantar cin zarafi mafi muni daga Dakarun kai daukin gaggawa na kasar

Wasu ‘yan gudun hijira da suka yi gudun hijira sun samu damar numfasawa bayan wani mummunan balaguron hijira da suka kwashe na tsawon kwanaki a kafa da suka bar komai nasu, don gujewa mummunan hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa ke kai wa kan kauyukan arewa da gabashin jihar Aljazira da ke tsakiyar kasar. ‘Yan gudun hijirar sun ce sun fuskanci munanan cin zarafi da suka shafi maza da mata.

Ali Al-Numairi, wani dan gudun hijira daga gabashin jihar Aljazira ya ce: Dakarun kai daukin gaggawa ba mutane ba ne kuma ba su da wata dabi’a ta bil’adama, kuma suna aika duk abin da son ransu ya riya musu.

Sumayya Al-Hajj, wata mata da ta yi gudun hijira daga gabashin jihar Aljazira ta ce: Dakarun kai daukin gaggawa, sun yi wa mata fyade, sace-sace da kisan gilla tare da korar mutane daga gidajensu.

Ahmed Iraki, memba na ofishin yada labarai na taron jihar Aljazira, ya ce: A cikin kwanaki 21 da suka gabata, alkaluman sun kai sama da ‘yan Sudan 1,237 da aka kashe, kuma za a iya samun karin karuwar adadin wadanda aka kashe musamman a arewa da gabashin jihar Aljazira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments