Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kama ‘Yan Leken Asirin Isra’ila A Lardin Mazandaran Na Kasar Iran

Dakarun juyin jaya halin Musulunci ta Iran sun kama wani wakilin hukumar leken asirin Isra’ila Mossad a arewacin kasar Iran Dakarun kare juyin juya halin

Dakarun juyin jaya halin Musulunci ta Iran sun kama wani wakilin hukumar leken asirin Isra’ila Mossad a arewacin kasar Iran

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanar da kame wani jami’in hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila “Mossad” a lardin Mazandaran (arewacin kasar Iran), wanda ke shirin kai harin ta’addanci a cikin kasar.

Sanarwar da dakarun kare juyin juya halin suka fitar ta bayyana cewa: wani ma’aikacin fage na makiya da ke shirin aiwatar da ayyukan ta’addanci ta hanya kai tsaye wajen jagorantar masu adawa da Iran a kasashen waje, an kama shi ne a wani gagarumin samame da jami’an leken asirin na Karbala suka kai, kafin ya aiwatar da duk wani aikin ta’addanci.

Sanarwar ta kara da cewa: Bincike ya kai ga gano tare da kama wasu da dama daga cikin ‘yan kungiyar leken asirin da lamarin ya shafa.

Tawagar masu leken asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci a lardin Mazandaran ta tabbatar da cewa tana cikin shiri da kuma taka tsantsan, kuma ta yi gargadin cewa “duk wani mataki na nuna adawa da tsaron kasar, zai fuskanci dauki mai tsauri da raɗaɗi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted