Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwa a ranar 16 ga watan Agusta na tunawa da dawowar fursunonin da aka ‘yantar zuwa mahaifar ta daular Musulunci. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Fursunonin da aka ‘yantar madaukaka, sune ainihin bayyanar gwagwarmaya da tsayin daka na ruhi da kuma bege na dabaru.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 16 ga watan Agusta na bikin tunawa da dawowar ‘yantattun fursunoni (fursunonin yakin shekara ta 1980-1988 a yakin da aka kakaba kan Iran), da tunawa da yakin kwanaki 12 da ‘yan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran da kuma tunawa da gwagwarmayar Falasdinawa. Haka nan kashin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta sha da masu goya mata baya musamman Amurka a wannan yanki, sun kasance gwagwarmaya na hakika da suka nuna kwarewar mujahidai ta tabbatar da cewa; ƙarfin Imani ne da haɗin kai na ƙasa, da tsayin daka na juyin juya hali na iya murkushe manyan injunan yaƙi da manufofin mulkin mallaka.”
Sanarwar ta kara da cewa: Wadannan jarumai ba wai kawai sun dakile makircin makiya Ba’ath da masu mara masa baya na yammacin duniya da Gabashi ba ne saboda da jajircewar ‘yan gwagwarmaya a lokacin da ake tsare da su ba ne kawai, har ma bayan dawowar su, tare da kasancewarsu masu himma da zaburarwa a fagen ilimi, al’adu, gudanarwa, zamantakewa, sun zama karfi na baya bayan nan na manufofin Musulunci, da samar da ci gaba na juyin juya halin Musulunci, da kuma taka rawa wajen samar da ci gaba na juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran.”