Dakarun na kare juyin juya halin musulunc na Iran sun gudanar da atisyen ne dai a kwana na biyu wanda aka bai wa taken; “ Manzon Allah mafi girma” karo na 19 A gundumar Kerman dake yammacin kasar.
Birgediya janar Muhammad Nazar Azimi wanda shi ne kwamandan cibiyar dakarun kare juyin ta Najaf- Ashraf, ya bayyana muhimmancin wannan rawar dajin inda ya ce:
“ Manufar wannan rawar dajin ita ce zama cikin shirin yaki.”
Ana yin wannan rawar dajin ne dai a yankin Oramanat da kuma Ozgaleh dake kan iyakar Iran ta yamma. Sai dai har ya zuwa yanzu ba a bayyana nau’in makaman da ake amfani da su ba a wajen rawar dajin