Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun nuna daya daga cikin rumbun ajiyar makamai masu linzaminsu na karkashin kasa wanda suka sanyawa suna ‘birnin makamai masu linzami’.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan dakarun na IRGC Janar Hussain Salami tare da Janar Amir Ali Hajizadeh kwamnaton bangaren tsaro sararin samaniya na rundunar suna fadar haka a jiya Jumma’a.
Tashoshin talabijin ta kasar Iran sun nuna makamai masu linzami samfurin Emad, Qadr da kuma Qiam wadanda suke amfani da makamashin ruwa-ruwa na daya daga cikin sansanonim.
Labarin ya kara da cewa, rundunar bata nuna kashi 90% na sauran rumbunoninta ba saboda matsalolin tsaro. Sannan sun ce Iran ta yi amfani da wadannan makamai masu linzami a hare-harem wa’adussadik na Farko da na biyu kan wuraren soje na HKI a cikin watan Afrilu da kuma Octoban shekarar da ta gabata.
Tashoshin talabijin na labarai a nan kasar Iran suna kiran makaman da sunan ‘narkakkun duwatsu” kuma suna iya tashi a cikin dan karimin lokaci don wargaza anniyar duk wanda yake nufin JMI da sharri.
Janar salami ya yabawa dakarun IRGC da shiga cikin yake-yaken guda biyu, inda suka kai wa HKI hare-hare a shekarar da ta gabata. Sannan ya kammala da cewa farfagandar makima na cewa JMI ta rasa karfinta na makamai masu linzami ba gaskiya bane. Yace dakarun IRGC su na samar da makamai masu linzami dai-dai da zamani.