Dakarun kare juyin juya halin nmusulunci IRGC reshen ruwa ko Navy sun bada labarin cilla makamai kan kataparen tankunan dakon danyenman fetur guda biyu a mashigar ruwa ta Hurmuz a jiya Litini, bayan da suka rudu da umurnin Amurka na su wuce ta mashigar ba tare da neman izini daga sojojin Iran a yankin ba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar IRGC ne cewa jiragen biyu sun kashe na’urorin gane inda suke wato GPS sannan suka kama hanyar wucewa ta mashigar, wanda ya kai ga lalatasu da kuma hanasu wucewa kwatakwata.
Kakakin rundunar Khatamul Anbiya(s) Kanar Ibrahim zulfikar ya bayyana cewa jiragen ruwan sun yi kokarin wucewa da mashigar ne bayan da shugaban kasar Amurka Donal trump ya bada sanarwan karban iko da mashigar ruwa ta Hurmuz.
Yarjeniyar da Amurka da JMI suka cimma a yarjeniyar Islamabad da kuma wacce Trump da Pezeshkiyan sukasanyawa hannu a watan Afrilun da ya gabat duk sun amince da cewa ikon mashigar ruwa ta Hurmuz na hannun gwamnatin JMI. Ya kara da cewa, yin watsi da wannan yarjeniyar da Trump yayi a taron NATO na turkiyya bai tada ita daga aiki ba.