Dakarun kare juyin juya halin musulunci, IRGC, sun nuna daya daga cikin sansanin jiragen ruwan yaki masu sauri a karkashin kasa a karo na farko.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa babban kwamandan IRGC burgediya Hussain Salami, tare da rakiyar kwamandan sojojin ruwa Rear admiral Alireza Tansiri ne suka nuna sansanin jiragen ruwan yaki.
Labarin ya kara da cewa jiragen ruwan yakin wadanda suke saurin kilomita kimani 200 a ko wace sa’a, ya na iya damar cilla makamai masu linzami masu yawa a kan makiya a lokacinda yake tafiya.
Janar salami ya bayyana cewa sansanin sojojin ruwan da aka nuna kadan ne daga irinsa da suka gina a karkashin kasa.
Dakarun IRGC dai suna shirye -shirye ne na tunkarar duk wata barazana da zata zowa kasar daga makiyanta, musamman HKI wacce ta kaiwa kasar hare-hare a shekarar da ta gabata. Sannan a yanzun ma, tana baranar zata sake yin hakan.