Dakarun kare juyin juya halin Musulunci a nan Iran IRGC sun fidda sanarwa ta musamman don taya, al-ummar Falasdinu murnar nasarar da suka samu a kan HKI bayan yaki da hakuri da bada shahidai na kimani watanni 16 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sanarwan taya murnar ta na cewa: Falasdinawa sun tabbatar da matsayisu a tsawon tarihin bil’adama kan hakuri da suka yi na yakar HKI, yan amamaye na tsawon wattani kimani 16.
A ranar Laraban da ta gabata ce, aka bada sanarwan tsagaita wuta, da kuma kawo karshen yakin, ta bakin firai ministan kasar Qatar Mohammad bin Abdurrahman bin Jasim Ali – Thani a birnin Doha na kasar Qatar. Kuma an cimma tsagaita wutar ne saboda kai kawon jami’an gwamnaton Qatar da kuma na kasar Masar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce yarjeniyar zai fara aiki ne a ranar Lahadi mai zuwa, 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025. Banda haka za’a aiwatar da yarjejeniyar ne a cikin matakai uku da kuma kwanaki 42.
Banda tsagaita budewa juna wuta dai, akwai musayar fursinoni, inda daga ciki har da sakin fursinonin Falasdinawa 1000 wadanda yahudawan suke tsare da su a Gaza, daga cikinsu har da wadanda suke cin kaso na lokaci mai tsawo.
A marhala ta farko dai, bangarorin biyu zasu saki, fursinoni 33 wadanda suka hada da yara kanana, sojoji mata, da wadanda suke da shekaru 50 zuwa sama, sannan da marasa lafiya da wadanda suka ji rauni.
Sannan Bayan haka, akwai janyewar sojojin HKI daga gaza a mataki- mataki.
Majiyar ta IRGC ta bayyana cewa an tilastawa HKI dakatar da bude wutan, ba da sonsu ba. Don haka wannan tsagaita wutar a wajensu ba karamin kaskanci ne ba.