Search
Close this search box.

Gaza: Falastinawa fiye da 100 Sun Yi Shahada A Safiyar Yau A Wani Harin Isra’ila

Mummunan kisan kiyashi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a safiyar Asabar a lokacin da ta kai harin bam a wata makaranta da ke

Mummunan kisan kiyashi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a safiyar Asabar a lokacin da ta kai harin bam a wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar Al-Daraj da ke tsakiyar birnin Gaza, ya yi sanadin shahadar Falastinawa sama 100, tare da jikkatar wasu da dama.

Yayin da hare-haren ta’addancin da take kaiwa zirin Gaza ya shiga kwana na 309, haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake yin wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a yau inda ta kai hari a makarantar Al-Tabaeen da ke unguwar Al-Daraj da ke tsakiyar birnin Gaza, da ke dauke da ‘yan gudun hijira.

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar da cewa “dakarun” mamaya sun yi wani kisan kiyashi a cikin makarantar “Al-Tabaeen”, inda mutane fiye da 100 suka yi shahada wasu da dama kuma suka jikkata.

Bayanin ya kara da cewa, “Saboda ta’addancin kisan gilla da kuma yawan shahidan, kungiyoyin likitoci, da masu bayar da agajin gaggawa, ba su iya kai dauki ga dukkanin wasdanda suka jikkata ba da kuma tattara gawarwakin dukkan shahidan.”

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya yi Allah wadai da wannan kisan gilla da kakkausar murya, tare da yin kira ga duniya da ta yi Allah wadai da shi, tare da dora alhakin hakan a kan mara baya da gwamnatin Amurka ke yi ido rufe ga gwamnatin Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments