Colombia Ta Bukaci Taron Gaggawa Na Kwamitin Tsaron Na MDD Kan Abinda Ya Faru A Venezuela

Gwamnatin kasar Colombia ta bukaci taron gaggawa na kwamitin tsaro na MDD dangan da hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Venezuela da kuma sake

Gwamnatin kasar Colombia ta bukaci taron gaggawa na kwamitin tsaro na MDD dangan da hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Venezuela da kuma sake shugaban kasa Nicolas Madoro da kuma matarsa.

Har’ila yau gwamnatin kasar ta Colombia ta kara taron gaggawa na kungiyar kasashen Laten Amurka da Carebian (SILAK) har ‘ila yau da taron ministocin harkokin wajen kasashen na SILAK.

Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar gwamnatin kasar ta Colombia na fadar haka a yau Lahadi. Ta kuma kara da cewa a gobe litinin ne kwamitin tsaro na MDD zai zauna don tattauna wannan batun.

A jiya Asabar da safe ne sojojin kasar Amurka suka kutsa cikin kasar Venezuela suka kuma kai hare-hare kan wasu jihohi a kasar sannan suka sauka cikin fadar shugaban kasa suka kashe masu gadin shugaba madoro suka shiga fadar suka kuma kama shi da matarsa, suka tafi da su Amurka.

Tashar talabijan ta CNN ta bayyana cewa sojojin Amurka da ake kira ‘Delta Force’ na sirri ne suka kai hare-hare kan wasu jihohi a kasar ta Venezuela da kuma babban birnin kasar inda ta yanke wutan lantarki da intarenat da wasu yankuna a birnin sannan suka saka a cikinm fadar shugaban kasa suka kama shi da matarsa suka tafi da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted