Jakadan China a Iran ya ce kasarsa za ta dauki mataki idan takunkumin da aka sanya wa Iran ya shafi muradun ta.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Tehran jami’in diflomasiyyar naChina ya ce Beijing “ba za ta yi jinkirin daukar mataki ba” idan sabbin takunkumin suka shafi cinikayyarta da Iran.
Wadannan kalamai sun zo ne a matsayin martani ga tambayoyi game da matsayin China kan takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da aka sake kakaba wa Iran, wanda aka sake kakabawa a karshen watan Satumba bayan da kasashen Turai da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 suka zargi Tehran da gaza cika wajibcin da ke kanta a karkashin yarjejeniyar.
Jakadan Chinar ya kuma nuna cewa Beijing na sha’awar karfafa hadin gwiwa da Tehran, yana mai nanata cewa Iran da China suna da ra’ayi daya kan ra’ayin hadin gwiwa a duniya.
China ita ce babbar abokiyar cinikayyar Iran, tana sayen kashi 29% na jimillar man fetur da Iran ke fitarwa.
An kiyasta cewa sama da kashi 92% na man fetur din Iran ana fitar da shi zuwa China, duk da tsauraran takunkuman Amurka.
Jimillar cinikin da China ke yi da Iran, gami da sayen man fetur, ya kai dala biliyan 65-70 a kowace shekara.
Masana sun yi imanin cewa China ta dogara ne da samar da mai mai araha daga Iran don tallafawa ci gaban masana’antarta.