Wakilin kasar China a MDD ya bayyana damuwar kasarsa akan yadda aka shigar da ‘yan ta’addan kasashenwaje cikin jerin wadanda aka bai wa manyan makaman soja a kasar Syria.
Haka nan kuma jakadan China a MDD ya nuna yadda kasar tasa ta damu da yadda Isra’ila ta kwace iko da wasu sassa na kasar ta Syria, tare da yin kira da a girmama ‘yanci da hurumin kasar.
Jakadan China a MDD Fu Kung ya ce; Da akwai damuwa akan yadda aka bai wa shugaban kungiyar musulunci ta Turkistan ( dan asalin kasar China) mukami a cikin ma’aikatar tsaron Syria, tare da yin kira ga Syria da ta yi aiki da fada da ta’addanci sannan kuma da hana amfani da kasar Syria a matsayin cibiyar ta’addanci akan kasashe.
Haka nan kuma ya yi ishara da bayanin bayan nan da kwamitin tsaro ya fitar akan Syria, yana mai yin kira ga dukkanin kasashe da su yi fada da dukkanin kungiyoyin da sunayensu su ka fito a karkashin na ‘yan ta’adda da kuma hana su samun wata mafaka a duniya.
Dangane da kutsen da HKI ta yi a cikin Syria,jakadan na kasar China a MDD ya yi kira da a girmama hurumi da ‘yancin kasar ta Syria,sannan kuma da wajabcin aiki da kudurorin MDD akan yankin tuddan Gulan da yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ta 1974.
Fu Kung ya bayyana goyon bayan kasarsa akan yadda ‘yan kasar Syria suke jagorantar tafiyar da siyasar kasar kamar yadda yake a karkashin kuduri mai lamba 2254.