China ta nuna damuwa game da tsoma bakin Amurka a harkokin cikin gida na Iran

China ta nuna adawa da tsoma bakin Amurka a harkokin cikin gida na Iran, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hari

China ta nuna adawa da tsoma bakin Amurka a harkokin cikin gida na Iran, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hari kan Jamhuriyar Musulunci don goyon bayan masu tayar da zaune tsaye da Isra’ila ke marawa baya.

“Ko yaushe muna adawa da tsoma baki a harkokin cikin gida na wasu kasashe kuma muna kira ga bangarorin da su mutunta ‘yancin kai da mutuncin dukkan kasashe,” in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China Mao Ning ga manema labarai a Beijing ranar Litinin.

“Muna adawa da amfani da karfi ko barazanar amfani da karfi a huldar kasa da kasa,” in ji Mao, yana mai cewa, “Muna kira ga dukkan bangarorin da su yi aiki ta hanyoyin da suka dace da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.”

Jami’in diflomasiyyar China ya kara da cewa Beijing “na fatan gwamnatin Iran da al’ummarta za su shawo kan wahalhalun da ake ciki a yanzu da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a kasar.”

Wannan jawabin ya zo ne yayin da Trump ya ce gwamnatinsa tana matukar bibiyar halin da ake ciki a Iran “.

A halin yanzu, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana halin da ake ciki a yanzu a matsayin “yakin ta’addanci.”

” Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce kungiyoyin ‘yan ta’adda sun kai hari kan gine-ginen gwamnati, ofisoshin ‘yan sanda, da shaguna.

Ya jaddada cewa hukumomin Iran suna da hotuna da ke nuna makamai da ake rarrabawa tsakanin masu zanga-zangar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted