Kasashen duniya sun fara yaba wa kasashen Amurka da kuma Iran, kan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi.
Kasashen Faransa, Jamus, Turkiyya, Rasha, Qatar da Oman da Ukraine China da Indiya duk sun yi maraba da cimma yarjejeniyar suna masu fatan bangarorin zasu mutunta yarjejeniyar.
Shugaban aksar Faransa E. Macron, ya ce yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma abun yabawa ce amma akwai babbar damuwa game da halin da ake ciki a Lebanon.
Shi kuwa firaministan Spain ya ce bai zai yada matsayin da wadanda suka jefa duniya cikin yaki ba.
Ita ma MDD, da kungiyar tarayyar turai, da kungiyar kula da sufirin jiragen ruwa ta duniya da kuma jagoran mabiya darikar katolika ta duniya sun yada da cimma yarjejeniyar.
A ranar Juma’a ake sa ran kasashen biyu zasu hadu Islamabad domin cimma yarjejeniyar karshe.
Matakin dai na zuwa ne bayan da shugaba Donald Trump, na Amurka ya soke matakin kai hari kan cibiyoyin makamashi da gadoji da kuma ruguza duk wani ci gaba na Iran muddin Iran ba ta amince da bude mashigar ruwa ta Hormuz ba.
Trump, ya wallafa a shafinsa na Truth Social, cewa : bayan tattaunawa da firaministan Pakistan da kuma babban kwamandan sojin Pakistan wadanda suka bukace ni da in dakatar da hare hare kan Iran, bayan da Iran ta amince da bude mashigar Hormuz, da kuma tsagaita wuta.