Hukumar kula da makamashin nukiliya ta iran, ta sanar cewa wani harin kawancen Amurka da Isra’ila ya yi sanadin shahadar mutum ma’aikaci guda.
Harin na safiyar ranar Asabar, ya kuam lalata wani banagre na cibiyar ta Bushehr, saidai babu wata barna da aka samu a babban bangare na cibiyar wanda ya tsaida aikin cibiyar.
Wannan shi ne hari karo na hudu da kawancen isra’ila da Amurka ke ka iwa cibiyar nukiliyar ta Bushehr tun bayan kaddamar da ayki kan iran.
Ko baya ga hakan hukumomin iran sun ce Amurka da isra’ila sun kai jerin hare hare kan wasu cibiyoyin samar da man fetur na iran.
Wannan dai na zuwa ne bayan alwashin da shugaba Donald Trump na Amurka ya sha na kaddamar da hare hare kan cibiyoyin makamashi na iran ciki har da na wutar lantarki muddin ba ta amince da yarjejeniyar da ya gabatar ba.
Masana da dama na gargadin cewa kai hare hare kan cibiyoyin makamashi na farar hula sabawa dokokin kasa da kasa ne kai tsaye kuma tamkar aikata laifukan yaki ne.