Mai magana da yawun gwamnatin Burkina Faso ya bayyana jiya litinin cewa ba su da bukatar kodinetan majalisar dinkin duniya a cikin kasarsu, biyo bayan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya zargi kasar da cin zarafin yara.
Kakakin ya ce a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu kwafinta, cewa “Hukumomi a Burkina Faso ba su shiga cikin shirya rahoton na Majalisar Dinkin Duniya mai suna Rikicin Yara da Makamai a Burkina Faso ba, kuma ba a sanar da su sakamakon binciken kafin wallafa shi ba.”
Gwamnatin Burkina Faso ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da yin “zargin da ba su da tushe da kuma yin karya a cikin rahoton, ba tare da ambaton binciken da ya dace ko kuma hukuncin kotu ba.”
A baya dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da zargin “kisa, cin zarafi, da kuma sace yara” a yankin Sahel, da kuma daukar yara aikin soja.
Gwamnatin Burkina Faso na Kallon irin wadanann matakai matsayin wani salo na siyasa domin bakanta sunanta a duniya, wanda kuma yana da alaka ne da matsayar kasar kan batutuwa na kasa da kasa.