Search
Close this search box.

Biden Ya Tabbatar Da Cewa Makamai Masu Linzamin Iran Sun Halaka Sojojin Amurka A Sansanin Sojojinta Da Ke Ainul Asad, Amma Trump Ya Boye Hakan

A yayin muhawar tsakanin shugaba Biden da abokin hamayyarsa Donal Trump, ya zarge shi da kariya ga Amukawa kan cewa ba sojan Amurka da ya

A yayin muhawar tsakanin shugaba Biden da abokin hamayyarsa Donal Trump, ya zarge shi da kariya ga Amukawa kan cewa ba sojan Amurka da ya halaka a lokacinda sojojin Iran suka cilla makamai masu linzami kan sansanin sojojin kasar da ke ainul Asad a cikin kasar Iraki a cikin watan Jenerun shekara ta 2020.

Biden ya tabbatar da cewa makaman kasar Iran sun kashe sojojin Amurka da dama ba wai ciwon kai ne kawai kamar yadda shugaban Trump a lokacin ya fadawa duniya ba. Ba don kome ba sai don bayan son shiga yaki da kasar Iran a lokacin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin watan Jenerun shekara ta 2020 ne sojojin kasar Iran suka cilla makamai masu linzami kan sansanin sojojin Amurka da ke Ainul Asad a kasar Iraki bayan da shugaban kasar Amurkan ya bada umurnin kashe babban kwamandan rundunar Kudus ta JMI Janar shahid Kasim Sulaimani.

Shugaban bai mayar da martini kan kasar Iran kamar yadda ake tsammani ba, inji Biden, sai kawai ya ce ai hare haren basu kashe wani ba, kuma wasu sojoji ne kawai suka sami ciwon kai. Shuwagabannin biyu sun yi ta zargi juna da son jawo yakin duniya na 3.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments