Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baqaei, ya mayarwa sakataren harkokin wajen kasar Burtania martani kan zargin kasar Iran a matsayin mai tsokana a yake yake har guda 2 wadanda Amurka da HKI suka dorawa kasarsa a cikin watani 9 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Esma’il Baqaei yana maida martani wa sakataren harkokin wajen kasar Burtania Ed Milibanda a wani rubutun da yayi a shafinsa na X inda yake kiran Iran a matsayin ‘mai tsokana’ saboda ta hana Amurka da HKI mamayar kasar a yake yaken guda biyu.
Baqaei ya ce, wannan yana dai dai da maida wanda aka zalunta azzalumi, sannan azzalumin kuma mai gaskiya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce, tunda ya tabbata cewa kasar Burtania tana da hannu dumu dumu a kashe Iraniyawa a wadannan yake yake ba zata iya wanda kanta da wadannan maganganu ba.
Baqaei ya bayyana cewa wannan wani kari ne kan irin kiyayyar da gwamnatin Burtaniya takewa Iran na lokaci mai tsawo.
Daga karshe Baqaei ya ce, abinda Miliband ya fada dangane da Iran, kamar fadar cewa sojojin Nazi sune masu gakiya wadanda aka tsokana a yakin duniya na biyu sannan Burtania da kwayenta muka masu tsokana ne.