Babban Sakataren Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ya Ce; Kungiyar Gwagwarmaya Tana Ci Gaba Da Kara Karfi

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya jaddada cewa: Gwagwarmaya za ta ci gaba da karfinta kuma a shirye take ta fuskanci duk wata

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya jaddada cewa: Gwagwarmaya za ta ci gaba da karfinta kuma a shirye take ta fuskanci duk wata barazanar makiya

Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Na’im Qassem, ya halarci taron kasa da kasa karo na 13 mai taken “Gaza, alamar gwagwarmaya”, inda ya jaddada cewa: Harin daukan fansa na “Ambaliyar Al-Aqsa” ya dawo da martabar al’ummar Falastinu, tare da yin nuni da cewa, harin ya maido da lamarin Falasdinu sabo fil a duk fadin duniya, kuma ya haifar da gagarumin sauyi a fagen duniya, kamar yadda aka din ga gudanar da gagarumar zanga-zangar a kasashen yamma domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu da ke zaluncinta.

Sheikh Qassem ya bayyana cewa: “Yakin gwamnatin Isra’ila da Amurka kan Gaza kokari ne na neman tarwatsa Falasdinu, kuma shiri ne na aiwatar da kisan kare dangi da kuma kawar da sunan Falastinu daga taswirar kasa da kasa. Wannan ya zo cikin mahangar Imam Khumaini (Allah ya tsarkake ruhinsa mai tsarki) cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila annoba ce da dole ne a kawar da ita daga wanzuwa, saboda wannan gwamnati ta ‘yan sahayoniyya taron makiya ne masu ta’adi da tauye hakkin al’ummar Falasdinu.”

Jagoran ya ci gaba da cewa: Al’ummar Falastinu masu fafutuka kuma masu daraja da dukkan bangarorinsu, da suka hada da samarinsu, maza, mata, yara, jajircewarsu a fagen gwagwarmaya, abin alfahari ne ga al’umma kuma alama ce ta daukaka da zasu samar da makomar Falasdinu mai ‘yanci da zasu kafa kasarsu da Qudus ne babban birninta, idan Allah ya yarda.

Falasdinu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments