Babban Kwamnadan Rundunar Tsaron Juyin Juya Hali Ya Ce: Juyayin Jana’izar Jagoran Ya Nuna Girman Matsayinsa

Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Juyayin makoki da aka yi a jana’izar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Iran

Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Juyayin makoki da aka yi a jana’izar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Iran da Iraki sabunta alƙawarin ne ci gaba da bin tafarkin Jagora da ya yi shahada

Shafin yanar gizo na rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Sepah News, ya sanar da cewa: Babban Kwamandan IRGC ya fitar da wata sanarwa da ke nuna godiyarsa ga al’ummar Iran da wadanda suka shirya jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulunci da ya yi shahada (Allah ya tsarkake ransa mai tsarki). Ya jaddada cewa: Babban jana’izar da bankwana, wanda aka siffanta da soyayya mai zurfi kuma na miliyoyin mutane daga Iran da Iraki suka halarta, wani lamari ne da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi. Ya sake bayyana gaskiya mai haske kuma ya nuna wa duniya kololuwar soyayya da hadin kai tsakanin Jagoran da mutane.

Kamfanin dillancin labaran “IRNA”, wanda ya ambato gidan yanar gizon rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Sepah News, ya ruwaito cewa: Babban Kwamandan IRGC ya jaddada cewa dimbin jama’ar da suka halarci jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Seyyed Ali Khamenei, ya zama sabonta alkawari da tafarkin wannan Imam da ya yi shahada da kuma bayyana biyayya ga burin al’ummar Musulunci. Haka kuma ya nuna haɗin kan al’umma wacce a koyaushe take tsayawa kafada da kafada, da gaskiya da ‘yan’uwantaka, a ƙarƙashin tutar ja ta Imam Hussain {a.s}, kuma ta tsaya cak kamar wani dutse mai tsayi a kan sojojin kafirci da girman kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted